Kasuwanci
Kasashe masu arzikin man fetur za su kara adadin man da suke fitarwa – OPEC
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/04/DteVn_4WoAAho-Z.jpg)
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da sauran kasashe masu arzikin man fetur da ba sa cikin kungiyar, sun cimma yarjejeniyar kara adadin man da su ke fitarwa.
A baya dai kasashen da ke kungiyar ta OPEC sun rage adadin man da su ke fitarwa da akalla ganga dubu dari shida a rana.
Hakan ya biyo bayan wani taro da mambobin kungiyar ta OPEC da sauran kasashe masu arzikin man fetur da ba sa cikin kungiyar suka gudanar a jiya talata.
A yayin taron OPEC ta amince da mambobinta su kara adadin man da su ke fitarwa da akalla ganga miliyan biyu a duk rana kuma kasar Saudiya ce za ta ba da kaso mafi yawa.
You must be logged in to post a comment Login