Labarai
Kashim Shettima zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jajanta wa ‘yan kasuwar Singa

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jihar Kano domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwar Singer.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya ba shi wannan umarni, inda tawagar za ta tashi daga Abuja gobe domin isar da sakon jaje ga ‘yan kasuwar da suka yi asarar biliyoyin naira sakamakon gobarar da ta tashi a karshen mako karo na biyu cikin makonni biyu.
Gwamnatin tarayya ta ce za ta kuma yi alkawarin tallafin kudi domin taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da taimakawa jihar Kano wajen gaggauta bude kasuwar.
Daga cikin tawagar akwai Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; Sanata Kawu Ismaila; da kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi.
Haka kuma Ministan Harkokin Jin Kai, Bernard M. Doro, da Darakta-Janar ta NEMA, Zubaida Umar, na cikin tawagar.
You must be logged in to post a comment Login