Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

KASSOSA za ta gudanar da taron ta shekara a jihar Jigawa

Published

on

Kungiyar tsoffin daliban Kwalejojin Kimiyya ta jihar Kano KASSOSA ta shirya gudanar da taron ta na shekara a jihar Jigawa ba kamar yadda aka saba gudanarwa a jihar Kano.

A cewar kungiyar an kai taron jihar Jigawa ne domin baiwa ‘ya’yanta na jihar damar halartar taron.

Sakataren kungiyar na kasa Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da yayi da wakilinmu Umar Idris Shuaibu a wani bangare na shirye shiryen taron na shekarar 2019.

Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ya bayyana cewa za a gudanar da taron ne a ranar 25 ga watan Disamba a cibiyar Manpower Development dake garin Dutsen Jihar Jigawa.

Wakilinmu Umar Idris Shuaibu cewa an shirya gabatar da mukaloli da dama a bangarori daban-daban na rayuwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!