Kimiyya
KASSOSA: zamu hada hannu da gwamnati wajen yin garambawul a bangaren ilmin kimiyya.
Shugaban kungiyar tsoffin daliban kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa aji na 1990 Inijiniya Abubakar Ibrahim Khalil ya ja hankalin gwamnatin jihar Kano wajen magance matsalolin da suka dabai-baye sha’anin karatun kimiyya.
Injiniya Abubakar Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne yayin taron Sallah karama da kungiyar ta gabatar a dakin taro dake asibitin Aminu koyarwa na Aminu Kano.
A cewar sa akwai bukatar mayar da hankali sosai a bangaren ilmin kimiyya, saboda koma bayan da ake fama da shi a bangaren yayin da duniya a halin yanzu tafi karfi a bangaren na kimiyya.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin kula da marayu da walwala na kungiyar Malam Kabir Dalha Kabir ya bayyana bukatar dake da akwai wajen yin gidauniyyar tallafawa marasa karfi a wani mataki na jan sauran al’umma a jika.
A yayin taron kungiyar tsoffin daliban kwalejin kimiyya ta Dawakin Tofa aji na 1990, sun karrama daya daga cikin mamban su daya samu matakin karatu na Farfesa a sashen nazarin Injiniya dake jami’ar Bayero anan Kano Farfesa Ibrahim Abdullahi Panshekara.