Connect with us

Kimiyya

An shiga rana ta biyu a aikin horas da ma’aikatan Freedom Radio

Published

on

Hukumar gudanarwa ta Freedom Radio da Dala FM Kano, sun shiryawa ma’aikatansu horo a kan yadda za su rika wallafa labarai a kan shafukan yanar gizo da yin bincike a internet, da tantance sahihancin labarai a internet.

Ma’aikatan wadanda suka fito daga sassa daban-daban na tashoshin za su shafe tsawon kwanaki uku suna karbar horon.

Masu karbar horon sun nuna farin cikinsu a kan yadda mai bayar da horon Basheer Sharfadi ya ke nuna kwarewa, a yayin da ya ke koyawa yan jaridun sabbin hanyoyin wallafa labarai a kafafen sada zumunci. Sannnan sun godewa hukumar gudanarwa ta Freedom Radio da ta shirya bitar.

Rahoto: Kamilu Saminu Zawaciki

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!