Labarai
Kasuwanci: Buhari zai tura tawagar ministoci kasar Ghana
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin kafa tawagar ministoci da za su ziyarci kasar Ghana don warware matsalolin da ake samu tsakanin ‘yan kasuwar kasar nan da kuma hukumomin kasar Ghana.
Ministan kasuwanci da zuba jari wanda kuma shi ne zai jagoranci tawagar zuwa Ghana, Otumba Adeniyi Adebayo ne ya tabbatar da hakan bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja game da lamarin.
Ya kara da cewa za su ziyarci kasar ta Ghana tsakanin ranakun 31 ga watan Mayun nan da muke ciki zuwa daya ga watan Yuni mai kamawa.
Sauran wadanda suka halarci taron na jiya akwai karamin ministan harkokin kasashen waje Ambasada Zubairu Dada, da babban sakatare a ma’aikatar kasuwanci da zuba jari Dr Nasir Sani-Gwarzo, sai shugabar hukumar bunkasa harkokin zuba jari ta kasa Yewande Sadiku.
Sai shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare Abike Dabiri Erewa da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login