Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Sarkin Musulmi: Ku fara duban watan Shawwal a talatar nan

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli kan harkokin addinin musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci al’ummar musulmi da su fara duban jinjirin watan Shawwal a yau talata.

 

Hakan na cikin wata sanarwa ce da sakatare janar na majalisar koli kan harkokin addinin musulunci farfesa Salisu Shehu ya fitar.

 

Sanarwar ta bukaci al’ummar musulmi da su fara duban jinjirin watan a yau talata.

 

‘‘Idan Allah ya sa aka ga watan a yau talata to gobe laraba za ta zamo ranar sallah idan kuma ba a gani ba to za a cika azumi talatin’’ a cewar sa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!