Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Katsina: An ceto wasu mata da aka yi garkuwa da su

Published

on

Rundunar ‘yan sanda Katsina ta bayyana kashe wani da ake zargin barawon shanu tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a kan iyakar Katsina da Zamfara.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta jihar SP Gambo Isah ne ya bayyana sunayen wadanda aka ceto da suka haka hadar da Kausar Surajo ‘yar shekara 22 da Aisha Ibrahim ‘yar shekara 28.

Ya ce Kausar dai mazauniyar garin Dutsen safe low cost ne a yankin na Katsina sai Aisha wadda ita kuma mazauniyar garin Baure ce dake kauyen Batsarin jihar ta Katsina.

Kakakin rundunar ya kara da cewa an yi garkuwa da su ne tun a ranar 16 ga watan Nuwamban wannan shekara a kauyen Firji dake jamhuriyar Nijar, aka kuma kai su wani wajen da ake cewa Sambisa a jihar Zamfara.

Rundunar ‘yan sandan da suka hadar da runduar Operation Puff Adder a ranar 21 ga watan da ake ciki ne suka ceto matan.

Sannan an gano su ne a dajin Rugu dake tsakanin Katsina da Zamfara, kuma tuni aka fara gudanar da binciken dangane da al’amarin.

Rundunar ‘yan sandan ta jihar Katsina, ta kuma bayyana cewa, ta samu nasarar kama wani hatsabibin barawon shanu mai suna Amadu dan shekara 35 a yankin Fulani na Doma, a karamar hukumar Faskari wanda tuni aka harbe shi, inda ya mutu nan take.

Rundunar ta ce an kashe Amadu ne yayin da mutanensa ke yunkurin sace wasu shanu a Bayan Dutsi dake dajin Ruwan Godiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!