Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun yi awan gaba da wasu tagwaye

Published

on

‘Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a kauyen Gizawa da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun isa kauyen ne a daren jiya lokacin da jama’a ke tsaka da bacci, inda daganan ne su ka shiga wani gida, su ka sace tagwayen Hassana da Hussaina Idris.

Al’ummar garin sun shaidawa manema labarai cewa, ‘Yan bindigar sun shiga gidan wani mutum mai suna Magaji Abu a kauyen Badole, inda suka sace dabbobinsa gaba daya.

Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da mutane 8 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun sace dan kasuwa a Sokoto

Ana Samun yawaitan karuwar kai hare-hare yan bindiga dadi sakamakon makwaftaka da Zamfara

A wani labarin kuma rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina, ta ce, ta ceto wasu mutane shida wadanda ‘Yan bindiga suka sace su a baya-bayan nan.

Mai magana da yawun rundunar ‘Yan sandan jihar ta Katsina, SP Gambo Isah, ya ce, tun a shekaran jiya Laraba, su ka samu nasarar ceto mutanen bayan wani batakashi da su ka yi da ‘yan bindigar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!