Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano: mai amfani da kafafen sada zumunta ya zargi rundunar ‘yan sandan Kano da cin zarafinsa

Published

on

Wani kwararre a fannin kafafen sada zumunta jihar Kano, Bashir Bashir Galadanci ya kai karar  kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kano bisa zargin cin zarafinsa tare da take masa ‘yanci a matsayinsa na dan-Adam.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, Bashir Galadanchi ya zargi kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, da tsare shi ba bisa ka’ida ba, tare da azabtar da shi yayin bincike da kuma tursasa shi amsa laifin da bai aikata ba.

Idan za’a iya tunawa dai an kama matashin ne a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata bisa zarginsa da bayyana wasu bayanai da suka shafi rundunar ‘yan sandan ba tare da amincewarsu ba.

A wani bidiyo da ya dinga zagawa a kafafen sada zumunta na Internet, an nuna Bashir Galadanchi yana baiwa rundunar ‘yan sandan hakuri bisa laifin da ya aikata, tare da cewa tsohon kakakin rundunar ne ya dauki nauyinsa wajen kushe rundunar ‘yan sandan Kano.

A wata wasika da lauyan Bashir Galadanchi Abba Hikima ya aikawa kwamashinan ‘yan sandan jihar kano, ya bayyana cewa bidiyon da ya zaga gari na cewar Bashir din na bada hakuri ga laifin da ya aikata ya yi shi ne cikin matsi da takura.

Wasikar mai dauke da kwanan wata 25 ga wannan wata na Nuwamba ta bayyana cewar, an tsare shi ne na tsawon kwanaki biyar ba tare da wata takarda daga kotu ba, tare kuma da azabtar da shi, da jami’an tsaro na SARS suka yi bisa umarnin kakakin rundunar.

Haka kuma ya zargi DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da cewar ya tursasa shi ya bata sunansa da kansa da kuma hana belinsa, bayan dukan da ya sha har sai da jini ya fito ta kunnensa kamar yadda lauyansa ya bayyana.

Sun dai bukaci rundunar ‘yan sanda jihar Kano da ta bincikI al’amarin tare da daukar matakin da ya dace.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!