Labarai
Katsina: Yan sanda ta umarci jami’anta su bai wa makarantu tsaro

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta umarci jami’anta da su bai wa dukkanin makarantun jihar tsaron da ya kamata.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran rundunar a jihar DSP Abubakar Aliyu ya fitar a safiyar yau.
Sanarwar ta kuma ce kwamishinan yan sandan jihar Bello Shehu, ya ce umarnin na zuwa ne yayin wani zaman tattaunawa da rundunar ta gudanar kan yadda ake samun matsalolin sace dalibai a kasar nan.
Ya kuma ce hakan na zuwa ne kan umarnin da babban sefeton yan sandan kasar nan Kayode Egbetokun, ya bayar kan bayar da tsaron da ya kamata a makarantun kasar.
You must be logged in to post a comment Login