Connect with us

Kiwon Lafiya

Kawu Sumaila: kafafun yada labarai abokan tafiyar mulkin dumukaradiyya ne

Published

on

Tsohon mai taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan al’amuran majalisar wakilai ta kasa Kawu Sumaila ya bayyana kafafun yada labarai a matsayin abokan tafiyar da mulkin dumukaradiyya ako ina a Duniya.

Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin gudanar da rantsuwar sabbin shuwagabannin kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshan jihar Kano wanda aka gudanar a yau Alhamis.

Kawu Sumaila, wanda ya kasance shugaban taron ya kuma kara da cewa ta hayar tsayayyar kafar yada labarai ne kadai za’a iya tabbatar da mulkin dumukaradiyya a kowacce kasa a duniya.

da yake gabatar da nasa jawabin, sabon shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshan jihar Kano, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu, ya ce a lokacin mulkinsa zai tabbatar da walwalar ‘ya ‘yan kungiyar tare da samar musu yanayin aiki mai kyau.

kungiyar ta wakilan kafafen yada labaran sun zabi Ibrahim Garba a matsayin Shugaba da Mustapha Hodi a matsayin sakatare da sauran su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,890 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!