Labarai
Kebbi: Yan sanda sun kashe ƴan bindiga 3 tare da ƙwato bindiga da harsasai

Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta ce, jami’anta sun samu nasarar kashe wasu ƴan bindiga uku, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47 da harsasai da dama a yankin ƙaramar hukumar Shange da ke jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar, rundunar ta ce ƴansanda sun fafata da ƴanbindigar ne a yankin na Shanga tare da taimakon ƴan-sa-kai, sannan wasu sun tsere da raunuka.
Kakakin ya ƙara da cewa wasu ƴanbindigar sun kai hari a garin Kesan da ke Shanga ɗin dai, inda suka yi garkuwa da mutum ɗaya mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu mai shekara 25.
Ya ce, amma daga bisani ƴansandan sun bi ƴanbindigar, inda suka samu nasarar ceto mutumin, amma sun harbe shi a ƙafa.
You must be logged in to post a comment Login