Labarai
Kimanin yan cira ni 200 ake tsammanin sun mutu a tekun Baharrum
Hukumar kula da ‘yan-cirani ta duniya ta ce wasu bakin haure ‘yan afurka sama da dari biyu ake tsammanin sun mutu a tekun Baharrum.
A cewar hukumar ta IOM ‘yan-ciranin wadanda ake tsammanin mafi yawansu ‘yan kasar nan ne suna kan hanyar su ne ta zuwa kasashen Italiya da Spaniya.
Babban jami’in yada labaran hukumar a kasar Libya Christine Petre, ta ce jiragen kwale-kwalen da suka nutse a tekun sun bar gabar ruwan Azzawiyah da Alkhums da ke kasar Libya ne zuwa kasashen turai.
Jami’an tsaro da ke gadin gabar tekun kasar Libya sun bayyana cewa sun samu nasarar ceto wasu daga cikin ‘yan ciranin wadanda kuma sun fito ne daga kasashen Senegal da Nigeria da kuma Mali, yayin da kuma akwai wasu guda takwas da suka fito daga kasar Bangladesh sai kuma wasu biyu ‘yan kasar Pakistan.
Rahoton na hadin gwiwa da hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya da jami’an tsaro masu gadin gabar tekun Libya suka fitar, sun ce; har I zuwa yanzu akwai wasu mutanen sama da dari biyu da har yanzu ba akai ga gano inda su ba.