Labarai
Kisan Hanifa: Kotu ta aike da Abdulmalik Tanko zuwa gidan gyaran hali
Kotun majistire mai lamba 12 ta aike da shugaban makarantar Nobel Kids Academy Abdulmalik Tanko zuwa gidan gyaran hali a ranar Litinin.
Kotun ta aike da shi gidan gyaran halin tare da waɗanda suka haɗa kai wajen aikata laifin da suka haɗar da Hashim Isyaku sai Fatima Musa.
Alkalin Kotun mai shari’a Mahmud Jibrin ya ɗage sauraron ƙarar don bada dama wajen samar da wadattaun hujjoji tare da ƙara faɗaɗa bincike kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta buƙata ƙarƙashin kwamishinan shari’a Musa Lawan har zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu.
Tun da fari dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ce ta gabatar da waɗanda ake zargin a gaban kotun gidan Murtala bisa tuhumar su da laifin yin garkuwa da Hanifa Abubakar tare da kashe ta.
Tun a ranar 4 ga watan Disambar 2021 ne Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar a kan hanyarta ta dawowa daga makarantar Islamiyya tare da buƙatar kuɗin fansa da ya kai naira miliyan 6 bayan ya kashe ta.
You must be logged in to post a comment Login