Labarai
Ko kun san abinda yasa hukumomin kashe gobara ke fuskantar matsala?
Wani bincike da a baya-bayan nan aka gudanar ya bayyana cewa hukumar kashe gobara a jahohin kasar nan na fama da rashin wadatattun kayayyakin aikin da zasu kai agaji a yayin da wani ibtila’i ya afko.
Haka kuma binciken ya gano yadda Gwamnatocin jahohin basa mayar da hankali wajen ganin sun samarwa da hukumar wadatattun kayayyakin aiki da zasu ci gaba da ayyukan su cikin sauki
Daga cikin jahohin da binciken ya bayyana wadanda suke da karancin kayayyakin aiki a hukumar kashe gobara akwai jihohin Kano da Jigawa da Gombe da Kogi da Kebbi da Calaber da Anambra da Katsina da kuma Nassarawa da dai sauran su.
Binciken ya gano cewa daga cikin kayayyakin aikin da hukumar ta rasa akwai rigunan da kan taimakawa jami’an damar shiga don kashe gobara da kuma karancin ruwa mai dauke da sinadarin kashe gobara, da rashin na’urar da kan taimaka musu wajen shakar iska a yayin da suke aikin shawo kan wani ibtila’i har ma da karancin motocin sufuri.
Dole ne Al’umma su hada kai da hukumar Kashe gobara-Usman Alhaji
Majalisar wakilai na binciken kudaden da aka warewa hukumar kashe gobara
Gobara ta tashi a FCE dake Kano
Akan hakan ne wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta zanta da wasu mutane anan Kano, inda suka bayyana irin koma bayan da rashin wadatattun kayan aiki a hukumar ke haifarwa musamman a yayin da ake bukatar agajin gaggawa, suna masu cewar a gaskiya dole gwamnati ta tallafawa wannan hukuma kasancewar tana fuskantar kalubale daban-daban.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’id Muhammad Ibrahim ya bayyana cewa hukumar su bata da wata matsala ta kayayyakin aiki kamar yadda waccan rahoto ya bayyana inda yace a yanzu haka ma sun fi hukumar kashe gobara ta gwamnatin tarayya wadatattun kayan aiki.
Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta sake zantawa da wani mai fashin baki kuma shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Network for justice da ke nan jihar Kano, Dr Bala Abdullahi Gabuwama ya bayyana cewa koma baya ne ga jahohin kasar nan wajen kin samar musu da kayayyaki aiki musamman ma a hukumar kashe gobara.
Ya kara da cewa kasar nan ta ci gaba wajen gine-ginen benaye masu tsayi wanda kuma rashin kayayyaki da zai taimaka wajen dakile ibtila’i babban koma baya ne ga sha’anin mulkin kasa.
Dr Bala Abdullahi Gabuwama yace a bayyane yake bambancin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jahohi ko da kuwa a bangaren kasafin kudi, sai dai yace idan har jahohin suka jajirce to kuwa za su samar da fiye da abin tarayyar zata samar.