Rahotonni
Ko kun san yadda mata ke gudanar da hutun karshen mako?
Akasarin mata masu aiki da zarar aka ce karshen mako yazo to babu shakka kowace mace ta shiga wani farin ciki na daban saboda zata kasance cikin iyalan ta.
Daga cikin abubuwan da mutan ke yin tanadi akwai girke-girke da gyaran gida da kuma shirya fita da yara ko da mai gida.
Sai dai wasu matan kan yi korafin cewar mazajen su ba sa zama a gidaje ko da sun yi musu girke-girke don gudanar da hutun karshen mako.
Ga wasu matan abun ba haka yake ba don kuwa wasu mazacen kan zauna ne tare da matan don yin hutun karshen makon.
A dai karshen makon matan aure kanyi amafani dashi domin yin kitso, gyaran jiki na musamman da kuma ziyarce-ziyarce.
Sannan lokacin kan bada dama ga iyaye mata damar samun kulawa ta musamman game da ‘ya’yan su.
Hari la yau matan kanyi amfani da hutun wajen zuwa makarantun addini da kuma karin wasu makarantun na karatun zamani.
Binciken da Freedom Radio tayi ya gano cewa babban abinda mata musamman a jihar Kano suka fi maida hankali akai a karshen makon, shi ne bukukuwa, domin kuwa a wannan lokaci ne matan ke halartar bukukuwan aure tsakanin ‘yan uwa da kuma abokanan arziki.
Labarai masu alaka:
Wata matashiya ta yi yunkurin kashe kanta sakamokon auren dan shekaru 70
Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.