Connect with us

Rahotonni

Abinda ke ciwa mutane tuwo a kwarya a asibitin AKTH Kano

Published

on

Featured Video Play Icon
Latsa hoton dake sama domin sauraron cikakken bayanin cikin sauti.

Wani bincike da Freedom Radio ta yi ya gano yadda ake fama da matsala wajen tsarin karbar kudi a zamanance da ake kira da “Cashless Policy” a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Wato dai babu kyakkyawan tsari na zamani wajen biyan kudi daga masu mu’amala da asibitin ta tsarin POS.

A wannan zamani da muke ciki na takaita ta’ammali da kudade a hannun jama’a wato “Cashless Policy,” ana ganin hakan ba karamin koma baya bane ga asibitin koyarwa kamar na Aminu Kano.

Labarai masu alaka:

Kano: Masu fama da cutar koda sun roki gwamnati ta mayar da wankin Koda kyauta

Asibitin AKTH zai gudanar da jarabawar kwarewa ga likitoci fiye da dubu

A yanzu dai babu damar biyan kudi ta hanyar amfani da zamani a asibitin sai dai abi tsarin karbar zunzurutun kudi tsaba ta hannu-hannu.

Wannan tsari dai ya haifar da cunkuso a wurin biyan kudin domin kuwa sai mutum yabi dogon layi kafin ya samu biyan kudin aiki a asibiti.

Wakilin Freedom Radio Nasir Salisu Zango ya gano yadda hatta masu sayar da abinci a asibitin Malam Aminu Kano na amfani da na’urar hada-hadar kudi ta POS.

Koda yake Freedom Radio ta gano cewa akwai wanda ya kafa sana’ar cirar kudi ta na’urar POS din a harabar asibitin, amma hakan ya gagara samuwa a tsarin ta’ammali da hada-hadar kudi a asibitin na Aminu Kano.

Da wannan ne Freedom Radio ke shawartar hukumar asibitin kan tayi duba, don tausayawa al’ummar dake hulda da asibitin.

Labarai masu alaka:

Asibitin kashi na Dala ya fadakar da dalibai illar gobara

AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu

Addini

Matakai 4 don yaki da Coronavirus a musulunce – Sheikh Daurawa

Published

on

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu matakai hudu matsayin, hanyoyi kaifiyyan da za a bi kan annobar Coronavirus.

Malam Daurawa yayi wannan jawabi ne cikin hudubarsa ta yau jumu’a a masallacin sa dake unguwar Fagge Plaza.

Mataki na farko a cewar Malam Daurawa shi ne Imani da kaddara cewa abinda Allah kaddara shi ne zai faru, musulmi yayi Imani cewa mahalicci ne ke da ikon kaddara masa rayuwar sa.

Na biyu shi ne, mu yarda da hukuncin Allah na mutuwa ko rayuwa, don haka a duk sanda mutuwa ta zo sai mutum ya tafi ko da Coronavirus ko babu ita.

Mataki na uku, daukar matakan kariya, musamman abubuwan da jami’an lafiya suke ta fada, yakamata abi wadannan matakai sau da kafa.

Abu na hudu shi ne, jama’a ta kaucewa yada jita-jita, abubuwan da ake yadawa na karya game da Coronavirus sun yi yawa.

A lokacin annobar Ebola wani ya kirkiro cewa a yi wanka da gishiri, yanzu kuwa an yiwa Annabi (s.a.w) karya cewa wai wani mutum yayi mafarki ya ga manzon Allah (s.a.w) ya ce masa ya bude alkur’ani mai girma ya duba zai ga gashi, sai ya jika shi ne maganin Coronavirus.

Cikakken rahoton zai zo muku a shirin Inda Ranka na yau @9:30pm.

Karin labarai:

Covid-19: BUK ta umarci daliban dake zaune a makarantar su koma gidajen su

Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano

Continue Reading

Rahotonni

Shin kun san muhimmancin abun kashe Gobara-Fire Extinguisher

Published

on

Iftila’in gobara dai kan faru a lokuta daban-daban a cikin jama’a, musamman a lokaci na dari {Sanyi}wanda ke sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

A wani mataki na yin shirin ko-ta-kwana, da daukar matakin gaggawa   ta sanya kwararru suka kirkiro abin kashe gobara cikin gaggawa don yin  rigakafi na kasha wuta da aka fi sa ni da  Fire Extinguisher.

Muhimmancin abin kashe gobara na Fire Extinguisher ba zai misaltu ba, musamman ma a cikin gidaje da asibitoci da masana’antu, har ma a cikin ababen hawa ciki  da motoci da kasuwanni da sauran wurare.

Sai dai jama’a da yawa daga cikin mutane ba su san muhimmancinsa ba, a gefe daya  kuma ba sa tanadar sa don ajiyewa a kusa da su a matsayin kariya a matakin farko daga hadrin gobara.

Labarai maus alaka.

Kano: Gobara da hadura sun hallaka mutane da dama a watan da ya gabata

Gobara ta tashi a makaranta kwanan dalibai ta Kanwa

A lokuta da dama  amfani da abin kashe gobarar kan taimaka wajen rage asarar da ake tafkawa a lokacin gobara.

A ta bakin kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano,  Sa’id Muhammad Ibrahim, a wata zantawar sa da wakiliyar Freedom Radio, Binta Ibrahim Yakasai, yace  muhimmancin abin kashe gobarar na da yawa kwarai da gaske, musamman ma a lokacin da gobara ta afku.

Sa’id Muhammad ya kuma  ja hankalin al’umma da su tanadi abin kashe gobara  a duk inda suke, sannan kuma su rinka sabunta shi da zarar wa’adinsa ya kare, don kare rayuka da dukiyoyinsu.

 

Continue Reading

Labarai

Mutanen garin Bakalari sun koka kan masu kwasar Bahaya

Published

on

Al’ummar Kauyen Bakalari da ke yankin karamar hukumar Tofa a nan Jihar Kano, sun koka dangane da yadda wasu mutane ke jibge musu bahaya da suke kwasowa daga bangarori daban-daban na jihar Kano.

Jama’ar garin sun ce, wannan lamari dai, yana shafar lafiyar su dana iyalansu har ma dana dabbobinsu.

Har ila yau mazauna garin sun ce ya dau tsawon lokaci yana faruwa, inda masu kwasar bahayan ke debo shi daga cikin birni su kawo yankinsu su jibge sannan su busar da ita.

A cewar su bayan sun busar da bahayar, sai kuma su rika durawa a buhu suna sayarwa, wanda hakan kan haifar musu da cututtuka da dama.

Malam Safiyanu Idris Ramosin, shine shugaban masu sana’ar busar da bahaya a kauyen na Bakalari, ya shaidawa wakiliyar mu Maryam Muhammad Bawa cewa, sun dade suna wannan sana’a kuma al’ummar garin basu taba yi musu korafi akai ba sai wannan karon.

Mallam Safiyanu ya kara da cewa sama da mutane 200 ne ke samun rufin asiri ta hanyar wannan sana’ar tasu.

A nasa bangaren Mai Garin Janguza, Malam Hudu Ya’u, ya ce, shi abin yafi karfin sa, saboda masu aikin ba-hayar sune suka sayi filin da kudinsu.

Har ila yau, wakliyar mu Maryam Muhammad Bawa ta tunubi sarkin tsaftar jihar Kano, Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo wanda ya ce duk da yake gwamnati ce ta samar da wurin don gudanar da wannan sana’a, amma yadda su ke aikin, bai dace ba.

Freedom Radio ta tuntubi ma’aikatar muhalli ta jihar Kano kan wannan batu, inda mataimakin daraktan kula da gurbacewar muhalli a ma’aikatar Muhammad Baba Ahmad ya ce, akwai irin wadannan wurare guda hudu da gwamnati ta ware, sai dai an tsara gudanar da wasu ayyuka kafin fara gudanar aiki a wuraren

Alhaji Muhammad ya kuma ce nan ba da dadewa ba, mai’akatar za ta yi duk me yiwuwa domin daukar matakin dakile matsalolin gurbacewar muhallin da ke addabar al’ummar garin na Bakalari da ke kusa da Mahuwa sakamakon jibge bahayar.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,276 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!