Connect with us

Labarai

Koto ta yanke wa Murja Kunya hukunci bayan samunta da yin liki da taka Kudi

Published

on

Kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda, ta yanke wa Yar tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya hukuncin daurin wata shida ko biyan tarar naira dubu hamsin.

 

Hukumar EFCC ce ta kama ta bisa kunshin tuhumar wulakanta kudi yayin da ake biki inda ta yi likin Kudi kuma ta taka su.

 

Lauyan hukumar Barista Musa Isa shi ne ya gabatar da ita inda kuma aka karanto mata ta kuma amsa lifinta inda kotun kuma ta yanke mata hukuncin daurin wata shida ko tabiya naira dubu hamsin.

 

Haka kuma kotun ta umarceta wajen yin anfani da kafar da ta ke anfani da ita wajen zama jakadiyar CBN da EFCC ta rika yada bayanan da ke nuna illar wulakanta kudi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!