Connect with us

Labarai

Kotu : Ana zargin wani mutum da yin damfarar daloli a Kano

Published

on

Kotun majistiri dake zamanta a Gyadi Gyadi karkashin mai sharia Auwal Yusuf ta dage sauraron karar Malam Lurwanu Tasiu wanda ake zargi da damfarar wani kusan naira miliyan uku da zummar zai bashi Daloli da kuma laifin yi masa barazana.

Tun da farko sun kulla mu’amalar kudi ne a tsakaninsu cewa Lurwanu zai bashi Daloli shi kuma zai bashi kudin Najeriya miliyan uku, inda ya bukaci daya kai masa kudin karkashin wata bishiya dake cikin wani kungurmin Daji bayan yakai sai ya zagaye ya debe kudin.

A zaman kotun na yau bayan kotu ta karantowa wanda ake zargi wato Lurwanu laifukan da ake tuhumar sa dasu ya musanta, sai dai lauyansa Barista Hamza Sani Bawa ya bukaci kotu data cigaba da barin Malam Lurwanu a hannun beli.

Munyi kokarin jin tabakin lauyan masu kara domin jin hanzarin su amma sunki cewa komai dan gane da zaman kotun na yau.

Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito mai sharia Auwal Yusuf Sulaiman ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar biyar ga watan janairu mai kamawa domin cigaba da sauraron shariar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!