Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

El-Rufa’i ya yi tir da kai hari tsakanin Zaria zuwa Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi tir da  kai harin wasu ƴan bindiga sun tare kan titin Zaria zuwa Kaduna daura da makarantar horas da sojoji da ke Jaji cikin daren  jiya.

A cewar  Kwamishinan dake kula da tsaro da ala’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan lokacin da wakiliyar Freedom Rediyo Shamsiyya Haruna ke ganawa da shi  ta  wayar tarho da safiyar yau a cikin shirin ”An tashi lafiya” ya ce sun sami rahoton ‘yan  bindigar sun bude wuta da misalin karfe 2 na dare akan motocin dake bin hanyar Zariya zuwa Kaduna.

Samuel Aruwan ya ce gwamnatin Kano ta bada umarnin da a baiwa  wadanda abun  ya rutsa da su kulawar gaggawa a asibitin 44 da ke Kaduna.

A cikin ‘yan kwanakin nan ayyukan ‘yan bindiga ya kara ta’azzara a jihar ta Kaduna.

Ko da a makon da ya gabata  sai dai wasu masu garkuwa da mutane suka sace wasu ma’aikata a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana fargabar  kan yadda ayyukan ta’addanci ke kara ta’azzara a yankin Arewacin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!