Labarai
Kotu ta hana bada belin Abduljabbar Kabara
Babbar kotun shari’ar musulunci da ke Ƙofar Kudu ƙarƙashin Ustaz Ibrahim Sarki yola ta yi watsi da neman belin da lauyoyin Abduljabbar suka yi.
A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyoyin gwamnati sun gabatar da kansu, ƙarƙashin Barista Mamman Lawan Yusufari SAN.
Daga bisani suma sabbin lauyoyin Abduljabbar sun gabatar da kansu, ƙarƙashin Batista Suraj Sa’ida.
Lauyoyin malamin sun roƙi kotu kan a basu kwafin shari’ar da aka yi a baya, domin su yi nazari kasancewar yau suka fara bayyana a gabanta.
Sannan suka buƙaci masu ƙara su gabatar da shaidunsu.
Daga nan kotun ta waiwayi Lauyoyin Gwamnati waɗanda suka ce ba su da suka kan bayar da kwafin shari’a.
Game da gabatar da shaidu ma lauyoyin Gwamnati sun ce a shirye su ke.
Kotun ta bayyana cewar, tuni suka aika da kwafin shari’ar, sai dai lauyan Abduljabbar ya ce, ba su aka bai wa ba.
Baya ga wannan lauyan malamin ya nemi a basu belin wanda suke karewa, sai dai lauyan Gwamnati ya yi suka a kai.
A ƙarshe kotun ta ƙi amincewa da buƙatar bada belin.
Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron shari’ar zuwa 14 ga watan Oktoba mai kamawa.
You must be logged in to post a comment Login