Labarai
Kotu ta aika matashi da babansa gidan yari bisa zargin kashe Limami
Wata babbar kotun majlistare a Kano ta ba da umarnin tsare wani matashi da mahaifinsa, bisa hannu a zargin kashe wani fitaccen limami mai suna Mallam Sani Muhammad.
Yayin da ɗan Yusuf Haruna aka gurfanar da shi gaban shari’a kan tuhumar kisan kai, mahaifin kuma an gurfanar da shi ne gaban alƙali bisa zargin ɓoye ɗan, da kuma kare shi daga fuskantar kamu.
Da aka karanto shari’ar a gaban kotu yau Laraba, lauya mai gabatar da ƙara Barista Fatima Ado Ahmad ta yi zargin cewa a ranar 31 ga watan Disamban 2023 da misalin ƙrfe 7 na yamma, wanda ake ƙara ya far wa limamin mai shekara 45, inda ya caka masa wuƙa mai kaifi a baya, lamarin da kuma ya yi sanadin mutuwarsa.
“Sakamakon haka, Mallam Sani Muhammad ya ji mugun rauni, inda aka garzaya da shi Asibin Ƙwararru na Murtala Muhammad, kafin wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Lauya mai gabatar da ƙara, Fatima Ado Ahmad ta kuma yi zargin cewa a dai wannan ranar, 31 ga watan Disamba, an zargi mutum na biyu da ake ƙara, Haruna Sani da ɓoye ɗansa, bayan ya soki Mallam Sani har ya riga mu gidan gaskiya, abin da ya saɓ wa sashe na 167 na kundin fenal.
You must be logged in to post a comment Login