Kiwon Lafiya
kotu ta aika wa shugaba Buhari da Atiku takardar sammaci
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta aike da takardar sammaci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Atiku Abubakar bisa zarigin su da barnatar da kudin da ya haura naira biliyan daya lokacin yakin neman zabe.
Cikin kunshin karar da dan takardar jam’iyyar NRM Usman Ibrahim Alhaji ya shigar gaban kotun ya nemi da a soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Usman Ibrahim ya bukaci kotun da ta yi amfani da sashe na 91 (2) na kundin dokokin hukumar zabe na shekarar 2010.
Ya kuma ce akwai bukatar kotun da soke Buhari da Atiku da shiga cikin takarar saboda sun yi amfani da sama dai naira biliyan guda kowanne su yayin yakin neman zaben.
Haka kuma ya kara da cewa yana fata kotun za ta yi abin da ya da ce wajen aikewa da wadanda ake tuhumar takardar karar su kuma amsa gayyatar kotun, domin tuhumar su kan laifukan da suka aikata.