Labarai
Kotu ta aike da tsohon Manajan Daraktan Bankin PHB gidan kaso
Mai shari’a a babbar kotun jihar Lagos, Lateefa Okunnu ta aike da tsohon Manajan Daraktan Bankin PHB da ya durkushe, Francis Atuche gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin badakalar kudade.
Kotun ta yanke wa Atuche zaman gidan gyaran halin tsawon shekaru 12 sakamakon yin sama da fadi da kudi naira biliyan 25 da dubu dari 7 a bankin.
Haka shima tsohon Babban Jami’in Kudi a bankin na PHB, Ugo Anyanwa da aka samu da laifin sata tare da bada hadin kai wajen sace kudaden, zai yi zaman shekaru 10 a gidan gyaran halin.
Daga bisani kuma mai shari’a Lateefa ta wanke tare da sakin matar Manajan Daraktan Elizabeth Atuche sakamakon rashin samunta da laifi yayin gudanar da shari’a.
You must be logged in to post a comment Login