Labarai
Kotu ta ba da umarnin kama babbar sakatariyar hukumar ƙasa da safiyo ta jihar Kano
Wata babbar kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu anan birnin Kano, ta umarci kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ya kamo mata babbar sakatariya a hukumar kula da ƙasa da safiyo, Dr. Zainab Yusuf Buraje, sakamakon bijirewa umarnin Kotu.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta ce, babbar sakatariyar, Dr Zainab Yusuf Buraje, ta ki bin umarnin kotu wadda ta bukace ta, da ta ba da wata takardar shaida da ake shari’a, akanta.
A cewar alkalin kotun, duk da an turawa babbar sakatariyar da rubutacciyar wasika da ke neman bayani kan takardar shaidar, amma ba ta bi umarnin da kotun ta ba ta ba, saboda haka, ya umarci kwamishinan ƴan sandan Kano da ya kamata ya gabatar da ita gaban kotun, cikin mako ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login