Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

‘Yan kasuwar Filin Idi da gwamnatin jihar Kano ta rushe sun shigar da kara Kotu

Published

on

‘Yan kasuwar Filin Idi da gwamnatin jihar Kano ta rushe sun garzaya zuwa babbar kotun Tarayya dake Kanon, domin ta dakatar da gwamnatin jihar  da kwamishinan ‘Yan sanda da kuma Hukumar Tsara Birane da yin tasarrafi da guraran da aka rushe musu.

A Yau Juma’a ne Babbar Kotun Tarayyar karkashin mai shari’a Simon Amobeda ya bayar da umarnin dakatar da yin duk wani tasarrufi da FIlin Idin da aka rushe har sai anzo gaban kotu.

‘Yan kasuwar su kimanin 56, sunce ‘neman Odar daga kotun ya zama wajibi ne bisa zargin yinkurin baiwa wata cibiya daga Saudi Arebiya yin amafani da filin Idin da aka rushe’.

Jim kadan bayan kotun ta bayar da Umarnin ne, Lauyan ‘Yan kasuwar Barista Nura Ayagi, ya ce sun garzaya kotun ne domin tausayawa masu kananan sana’oi da masu kasuwanci a wajen.

Rahoton: Yusuf Ali Abdallah

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!