Labarai
Kotu ta bada belin Alhassan Ado Doguwa
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gyadi-gyadi ta bada belin Alhassan Ado Doguwa.
Kotun ta bada belin Doguwa ne karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Yunusa Nasir.
Lauyansa Barista Nuraini Jimoh sune suka shigar da ƙara inda suke ƙalubalantar ƴan sanda da kuma kotun da aka karanto masa tuhumar.
Guda daga cikin Lauyansa ya bayyanawa kotun cewar akwai kura kurai wajan gurfanar da shi domin kuwa kotun da aka kai shi ƙarama ce ba ta da hurumin sauraren shari’ar.
Har ma ya kafa hujja da wasu sashi na kundin doka.
Haka kuma lauyoyin sun gabatarwa kotu takardar rashin lafiyar Alhassan Ado Doguwa.
Kotun ta gamsu da hujjojin su, inda ta sanya shi a hannun beli bisa sharaɗin mutane biyu na farko Sarki nai daraja ta ɗaya da kuma babban sakataren, sannan kuma zai ajiye katinsa na fita ƙasashen waje, kuma an haramta masa zuwa mazabarsa yayin zaben.
Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Bakanoma ya tawaito cewa, kotun ta ɗage zaman Shari’ar zuwa 20/3/2023 domin ci gaba da sauraran shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login