Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ma’aikatan INEC na wucin-gadi sun yi barazanar kaurace wa aikin zaben gwamnoni

Published

on

Wasu ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar zabe Mai zaman kanta ta Nijeriya INEC a Jihar Neja, sun yi barazanar kaurace wa yin aikin hukumar a zaben gwamna da za a yi ranar 11 ga wannan watan da muke ciki na Maris.

A zantawar ma’aikatan wucin-gadin da manema labarai, sun ce ba a biya su alawus-alawus na horo da na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da suka gudanar ba a ranar 25 ga watan jiya na Fabrairu.

Haka kuma cikin nuna takaici, ma’aikatan sun yi ƙorafin cewa duk da tsananin damuwa da barazana ga rayuwarsu, har kawo yanzu ba a biya su kudaden alawus-alawus din nasu ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!