Labarai
Kotu ta bada belin tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau
Kotun tarayya da ke zaman ta a nan Kano da bayar da belin Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da wasu mutane biyu daka gurfanar da su tare, akan wasu sharuda.
A zaman kotun na yau karkashin mai shari’a Zainab Abubakar Baji ta bayar da belin mutanen uku akan naira milyan dari kowannen su tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya musu, wadan da daya daga cikin su dole ne ya zama Darakta a matakin aiki a gwamnatin jiha ko ta tarayya.
Ha ka kuma cikin sharuddan kotun ta ce dole ne su ajiye wata kaddara a yankunan da kotun take da iko da shi a nan jihar Kano tare kuma da umartar su da su ajiye fasfunan su.
Kotun dai ta tuhumi tsohon ministan ilimin Malam Ibrahim Shekarau da karbar naira milyan 25 daga cikin naira milyan 950 da aka ce an bayar domin yakin neman zaben shekarar 2015 al’amarin da ya musanta.
Haka kuma a zaman kotun na yau ta sanya ranar 26 ga watan Yuni mai kamawa a matsayin ranar da za a ci gaba da saurarar karar.