Labarai
Kotu ta bada umarnin kamo mata Kabiru Turaki SAN
Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja dake Zaman ta a Maitama ta Bada umarnin a kamo Mata Barrister Kabiru Turaki SAN domin ya gurfana a gaban ta.
Da ya ke zartas da hukunci, a yau Alkalin kotun mai shari’a Keke Meke, ya ki amincewa da bukatar lauyoyin Kabiru Turaki da ke neman a ba su damar gabatar da wani kudiri a gaban kotun inda ya bayyana cewar, wanda ake kara ya na sane da cewar kotu za ta zauna yau, amma ya yi burus da kiran kotun.
Lauyan rundunr ‘yan sanda Barista Rabiu Umar ya soki lamirin lauyoyin Kabiru Turaki na kokarin sauya wani daftari da suka gabatar.
Kotun dai, ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 22 GA Watan gobe na Afrilu kafin nan yan sanda su kamo Kabiru Turakin Domin gurfanar da Shi kamar yadda kotun ta yi umarni.

You must be logged in to post a comment Login