Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Murja Kunya ta sake gurfana a gaban Kotu

Published

on

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Gyadi-gyadi karkashin jagorancin mai sharia Abdullahi Muhammad Liman ta yi umarnin a gabatar da murja Ibrahim kunya a gabanta.

Tunda farko lauyoyin murja ne suka shigar da kara suna karar hukumar Hisba da kwamishinan sharia na jahar kano da kuma kotun shariar muslinci ta PRP.

Lauyoyin Murja Kunya sun roki babbar kotun tarayya da a gabatar da murja a gaban kotun domin sun fahimci cewar anayi musu nuku-nuku.

Tun a baya kotun ta amince da rokon sai dai a zaman kotun na yau lautoyin gwamnati sun bayyana a gaban kotun ba tare da Murja ba.

Lauyoyinta sun bayyanawa kotun cewar lauyoyin gwamnati sun bijire wa umarnin kotun sai dai kotun tayi umarnin cewar a gabatar mata da murja cikin minti talatin.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai Murja Ibrahim Kunya na cikin kotun sakamako bin umarnin kotun da lauyoyin gwamnati suka yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!