Labarai
Kotu ta ci tarar hukumar KAROTA kan kama wasu da ta yi saboda sun yi goyo a babur
Babbar kotun jiha mai Lanba 14 ƙarkashin mai shari’a Nasir Saminu ta yanke hukunci dangane da shari’ar da wasu mutane uku suka shigar da suke kalubalantar hukumar KAROTA na kamasu da ta yi yayin da suka yi goyo a babur kuma aka ci tararsu.
A zaman kotun na ranar Litinin mai shari’a yayi karatun baya inda daga karshe kotun ta haramta kamen goyon da KAROTA ta yi musu, da kuma yankewa mutane tarar tunda ba baburin haya ba ne.
Kotun kuma ta umarci hukumar KAROTA da ta biya wadanda suka yi karar su uku Bello Basi Fagge da Lamin Ibrahim Adam da kuma Ibrahim Abdullahi za ta biyasu Naira dubu dari biyar biyar kowannensu.
Haka kuma za ta biyasu kudin kara Nairar dubu dari da kuma kudin da akaci tararsu Naira dubu bibiyu, kamar yadda wakilin Freedom Radiyo Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito.
You must be logged in to post a comment Login