Connect with us

Labarai

Kotu ta cigaba da sauraron shari’ar Malam Shekarau

Published

on

A yau ne babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano ta dage ci gaba da sauraran karar da ake tuhumar Malam Ibrahim Shekarau da wasu mutum biyu.

Babbar kotun tarraya dake zaman ta a kano taci gaba da sauraran karar da gwamnatin tarraya ke tuhumar Malam Ibrahim Shekarau da Aminu Bahir Wali da Mansur Ahmed da ake zargin su da sama da fadi da kimanin kudi naira miliyan dari tara da hamsin na jamiyyar PDP.

A cikin kudin Malam Ibrahim Shekarau ya karbi naira miliyan asirin da biyar da Mansur Ahmed shima ya karbi naira miliyan asirin da biyar daga cikin naira miliyan dari tara da hamsin.

Babban alkalin dake jagorantar karar Mai sharia Lewis Algbon na babbar kotun tarayya yace wanda ake zargi suna da damar kawo shedun da za su kare su.

Babban jamin dake wakiltar hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC yace kasha kudin baa bi kaidar daya kama ta ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,337 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!