Labarai
Kotu ta daure G. Fresh na tsawon wata biyar

Babbar kotun Tarayya mai lamba daya da ke zamanta a Kano ta yanke wa fitattacen mai amfani da kafar sada zumunta ta TikTok Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da G. Fresh, hukuncin dauri ko kuma biyan tara.
An dai gurfanar da shi a gaban kotun ne bisa zarginsa da cin mutuncin kudi.
Bayan karanta masa zargin ne kuma nan take ya amsa laifinsa.
Kotun ta aike da shi gidan gyaran hali na tsawan watanni biyar ko kuma ya biya tarar Naira dubu dari biyu.
An samu G. Fresh ne da watsa takardun kudi na Naira dubu-dubu a shagon Rahama Sa’idu da ke Tarauni yayin da su ke nishadi a junansu.
You must be logged in to post a comment Login