Labarai
Kotu ta gayyaci Diezani Alison-Madueke
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci tsohuwar ministar man fetur na kasar nan Diezani Alison-Madueke da ta gurfana gabanta don kare kanta kan zargin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke yi mata na halasta kudin haramun.
Alkalin kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta ba da umarnin bayan da lauyan EFCC Faruk Abdallah ya bukaci hakan.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu dai ta bukaci Diezani Alison-Madueke wadda ta tsere daga kasar nan bayan da ta sauka daga mukaminta a shekarar dubu biyu da goma sha biyar zuwa kasar Burtaniya, da ta gurfana gaban kotun don kare kanta kan tuhume-tuhume guda goma sha uku da hukumar EFCC ke yi akanta.
Wasu daga cikin zarge-zargen da hukumar ta EFCC ke yi ga tsohuwar ministar sun hada da: haramta kudaden haramun naira biliyan goma sha hudu da miliyan ashirin da tara da kuma wasu kudade naira biliyan uku da miliyan talatin da biyu.
You must be logged in to post a comment Login