Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutumin da ya fara zama lauya a arewa ya rasu

Published

on

Mutumin da ya fara zama Lauya a arewacin kasar nan kuma mahaifi ga gwamanan jihar Kwara, Abdurrahman Abdurrazak wato Alhaji Abdulganiyu Folorunsho Abdulrazak SAN ya rasu.

A cikin wata sanarwa da iyalan dattijon suka fitar sun ce, Alhaji Abdulganiyu Folorunsho Abdurrazak ya rasu ne da safiyar yau Asabar a birnin tarayya Abuja, yana da shekaru casa’in da uku a duniya.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daya daga cikin ‘ya’yansa Dr. Alimi Abdurrazak ta ce, mahaifin nasu ya rasu ne bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya da misalin karfe biyu na asubahi.

An dai haifi Alhaji Abdulganiyu Folorunsho Abdurrazak SAN wanda yake rike da sarautar Mutawali a masarautar Ilorin kuma Tafidan Zazzau a alif da dari tara da ashirin da bakwai.

Haka zalika sanarwar ta kuma ce ya rasu ya bar mai dakinsa Alhaja Raliat Abdurrazak mai shekaru casa’in tare da ‘ya’ya da dama ciki har da gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdurrahman Abdurrazak tare da jikoki da tattaba kunne da dama.

To Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa zunubansa in kuma tamu tazo Allah ya sa muyi kyakkyawar karshe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!