Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta kawo ƙarshen takaddamar iyakokin ƙasa da ke tsakanin Najeriya da Kamaru – Malami

Published

on

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kawo karshen taƙaddamar iyakokin ƙasa da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.

Attoni Janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan  a wata ziyara da ya kai wa  Jakadan majalisar dinkin duniya mai kula da Yammacin Afirka Mahamat Annadif.

Malami ya tabbatar da cewar kotun duniya ta kammala  yanke hukunci tsakanin ƙasashen biyu, ta hanyar fitar da iyakokin ƙasashen biyu kowacce akwai iya inda ta mallaka.

A nasa jawabin jakadan na majalisar ɗinkin duniya Annadif ya ce, majalisar za ta ci gaba da haɗa kan mambobin ƙasashen wajen ganin an samu kyakyawar alakar diflomasiyya da zaman lafiya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!