Labarai
Kotu ta nemi a kamo mata mai unguwa
Babbar kotun shari’ar Musulinci da ke zamanta a Kofar Kudu karkashin jagorancin mai shari’a Ustaz Ibarahim Sarki Yola, ya ba da umarnin kamo masa mai unguwar Gyadi Gyadi a duk inda yake sakamakon gaza bayyana a gaban kotu.
Umarnin kamo mai unguwar ya zo ne, bayan wani mutun da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya bai wa Sule Inda kudinsa naira miliyan tara akan wata mu’amalarsu da wani kamfani kuma mai unguwar ya tsaya masa har ya karbi belinsa a gaban kotu tun a zaman kotun na baya.
Sai dai a zaman kotun na yau Litinin 15 ga watan Maris 2021 bayan mai Shari’a Sarki Yola ya kira sauran bangaren wadanda ake kara don bayyana a gabansa amma ba su zo ba kuma mai unguwar Gyadi Gyadi da ya karbi belin wanda ake kara shima bai bayyana a gaban kotun ba a wannan zaman.
A nan take ne mai shari’ar ya bai wa Sufeto Sulaiman Sunusi umarnin kamo mai unguwar Gyadi Gyadin a duk inda yake kuma ya tsare shi sakamakon gaza bayyana da yayi a gaban kotun wanda yace hakan raini ne ga kotu.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa mai shari’a Ustaz Ibarahim Sarki Yola ya sanya ranar 22 ga watan da muke ciki na Maris domin cigaba da sauraron shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login