Labarai
Kotu ta rushe zaɓen Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC a Kano
Wata kotun tarayya da ke Abuja ta rushe zaben da aka yiwa shugaban jam’iyya APC tsagin gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje.
Tsagin gwamna Ganduje dai Abdullahi Abbas ne ya ci zaɓen da aka gudanar na jam’iyyar.
Mai shari’a Hamza Mua’zu ne ne ya rushe zaben a zaman kotu na ranar Talata.
Kotun ta tabbatar da zaben da aka yi tsagin tshohon gwamnan Kano Malam Ibrahim shekarau.
A cewar mai shari’ar zaben da aka gudanar tsagin Shekarau ya samu sanya samu amincewar mutum bakwai daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta aiko Kano domin gudanar da zaben.
Tun da fari dai ɓangaren tsohon gwamna Shekarau ya gabatar da ƙorafi ga kotu cewa tsagin gwamna Ganduje bai gudanar da zabe a matakin ƙanannan hukumomi da mazaɓu ba.
A watan Oktoba ne dai jam’iyyar APC ta gudanar da zaɓe shugabancin jam’iyya APC a Kano da sauran jihohin kasar, zaɓen da ya bar baya da ƙura ta ɓangarorin biyu, domin kuwa tsagin gwaman Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, yayin da tsagin Ibrahim Shekarau ya zaɓi Ahmad Haruna Zago a matsayin shugaba.
You must be logged in to post a comment Login