Inda Ranka
Kotu ta saida gidan wani mutum yana gidan gyaran hali
Duk da cewar bayan ya fito ya kai shigar da kara har ma kotu ta bada umarni amma hakonsa bai cimma ruwa ba, domin masu gwanjan babbar kotun jiha sun bujirewa umarnin ta
Wakilin mu Nasiru Salisu Zango ya rawaito cewa, a cikin kunshin bayanan shari’a wanda alkali Faruq na kotun kasuwa ya rubuta ya nuna cewa, irin hukunce-hukuncen da kotun ta bada umarni amma wadanda ake kara suka yi mirsisi a don haka kotun ta bayyana cewar matakin ya zama rainin-wayo.
Kamar yadda labarin ya nuna cewa wani mutumi ne wanda karayar arziki ta same shi har ta kai ga cin bashin da aka kai shi kurkuku saboda ya gaza
Wanda yana cikin wannan kadamin ne sai aka sake kai karar sa kotun kasuwar Kurmi saboda wadansu kudadan da ake binsa,duk da cewar an je wannan kotun kasuwar don tabbatar da sulhun da aka cimma a tsakanin su kama yadda hukuncin kotun ke tafiya akai, amma sai shari’ar ta sauya zane daga batun sulhu ta dawo karbar kudi.
Kai-tsaye : Yaushe ne za’a cigaba da sauraran shari’ar Ganduje da Abba?
Kotun daukaka kara ta sanya ranar shari’ar Ganduje da Abba
Kotu a Kano ta yankewa mai cin zarafin kananan yara hukunci
Haka shima wanda ake bi bashin Malam Bashir Fari Sharada ya bayyana cewa ,daga wannan ranar da kotun ta sulhuntasu bata kara neman sa ba, amma hakan alkali yayi hukuncin zuwa asayar da gidan sa ba tare da sanin sa ba.
Ya sake bayyana cewa, yana zauna ne da iyalin sa suna karin kumallo kwatsam sai sukaji an sako kai cikin gidan ana fatali da kayansu.
Akan haka ne Malam Bashir Fari Sharada ya bayyana bakin cikinsa duba da cewa wadanda aka je da su gidan shi har da Kurame domin ba za su iya jin irin roko da magiyar da yake musu ba,
Ya kara da cewar irin tozarcin da su kai masa har ma takai da iyalisa su kwana a makwabta shi kuma ya kwana a shagon damin acewar sa maganar siyar da gidan sa ta tabbata.
Hakan yasa ya daukaka kara shida lauyansa domin dakatar da Alkalin Sharif daukar matakin yanke hukuncin a baya, amma hakan bai samu ba saboda an dauke alkalin kotun wanda ya yanke hukuncin farko.
Amma kakakin babbar kotun jihar Kano Baba jibo Ibrahim ya ce alkalin babbar kotun jiha ya mayar da martanin cewa har idan wannan korafi yaje waje sa sai abin da ya tubewa buzu nadi.