Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

kotu ta sanya ranar cigaba da sauraron karar da masu nada sarki a kano suka shigar

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta saka ranar sha bakwai ga watan Disemba domin cigaba da sauraran karar da masu nada sarki a masarautar kano suka shigar da kara suna kalubalantar gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da wasu mutane bakwai akan kirkiro sababin masarautu hudu da akayi.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka shigar da karar sun hada da Alhaji Yusuf Nabahani madakin Kano, Alhaji Abdullhi Sarki Ibrahim Makaman Kano da Bello Abubakar Sarkin Dawaki mai Tuta da Alhaji Mukhtar Adnan Sarkin Ban Kano.

Masu nada Sarkin na Kano suna bukatar babbar kotun da ta umarci Gwamnan na Kano da a bar masarautar Kano yadda take.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!