Labarai
Kotu ta sassauta sharuɗan bada Belin Ɗansarauniya
Kotun majistret mai lamba 58 ƙarƙashin mai Sharia Aminu Gabari ta sassauta sharuɗan da ta gindaya a kan bayar da belin Injiniya Mu’azu Magaji Ɗansarauniya.
Yayin da yake bayyana matsayar kotun mai Shari’a Aminu Gabari ya ayyana cewar kotun ta amince da rokon lauyan kariya ta kuma sassauta sharuɗan belin, inda ta nemi ya kawo Limamin garinsu maimakon na Dawakin Tofa.
Kotun ta kuma umarce shi da ya biya gilashin motar gidan gyaran hali da aka fasa lokacin da aka ɗauki shi a motar.
An kuma umarci shi da yayi shiru da bakinsa.
Tun da farko kwamishinan ƴan sanda na Kano Sama’ila Shuaibu Dikko ne ya gurfanar da Ɗansarauniya bisa zargin cin mutunci da ɓata suna da kuma yunƙurin tayar da hankalin al’umma ta hanyar yada wani kirkirarren hoton gwamnan kyano Dr Abdullahi Umar Ganduje da wata mata a shafinsa na Facebook zarge zargen da Ɗansarauniyar ya musanta.
A baya dai kotun ta sanya Ɗansarauniya a hannun beli sai dai ya gaza cika sharuɗan da aka gindaya masa.
A zaman kotun na ranar Juma’a tawagar lauyoyin gwamnati ƙarƙashin Barista Khadija Aliyu umar sun hallara a gaban kotun.
Lauyan kariya Barista Garzali Datti Ahmad ya bayyana cewar takardun da suka zo da su kotu takardu ne na neman sassaucin sharaɗin belin da kotun ta sanya ya kuma bayyana cewar za su bi duk wani sharaɗi da kotun ta sanya matuƙar kotun ta karɓi roƙon su.
Anan ne kotun ta sassauta sharaɗin Belin.
You must be logged in to post a comment Login