Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Kano: Hisbah ta ɗauki limaman Juma’a aikin sa-kai

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ƙaddamar da kafata ina liman masallata kuma na jihar a matsayin dakarun Hisba na sa-kai.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.

“A yau Juma’a mun bai wa kowanne limamin masallacin juma’a a jihar Kano shaidar zama ɗan Hisba amma na sa-kai kasancewar aikin su yayi daidai da aikin hukumar mu” a cewar Ibnu Sina.

Ya ci gaba da cewa “Mun ƙaddamar da katin shaidar ne ƙarƙashin amincewar kowanne ɓangare da ya haɗar da wakilcin Izala, Tijjaniyya Ƙadiriyya kuma mun tattauna kan yadda za a ƙara inganta aikin”.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina ya kuma ce, an kusanto da limaman cikin hukumar ne don aikin ya ƙara ƙarfi tare da isar da saƙo cikin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!