Labarai
Kotu ta Umarci Abba Gida-gida ya biya diyyar wasu gine-gine da ya rushe a Kano
Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a jihar Kano ta umurci gwamnatin jihar da sauran wadanda aka yi ƙara, su biya wasu mazauna unguwar Salanta, kudi naira miliyan ɗaya kowannensu akan yunƙurin rusa musu kadarori ba bisa ƙa’ida ba.
Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin cewa yunƙurin gwamnatin Kano da jami’anta na sanya wa gidan Saminu Shehu Muhd da na Tasiu Shehu Muhd cikin jerin gidajen da za a iya rushewa bayan an buga musu lambar jan fenti ba tare da bin ƙa’ida ba, tauye ƴancinsu ne na mallakar kadara kamar yadda sashe na 43 da 44 na tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya tabbatar musu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Barista Bashir Ibrahim, wanda ya shigar da karar a madadin Saminu da Tasiu, bayan yanke hukuncin ya baiwa kotun bisa wannan hukunci, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta kare haƙƙi da martaba ƙimar ɗan’adam.
A nasa bangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano da sauran waɗanda aka yi ƙara a shari’ar, Barista Musa Dahuru Muhd daraktan shari’a a ma’aikatar shari’a ta Kano ya ce za su yi nazari a kan hukuncin tare da bai wa gwamnati shawara game da mataki na
gaba.
You must be logged in to post a comment Login