Labarai
Rikici : Kotu ta wanke mai Durin iskar Gas a Kano
Babbar Kotun Shari’ar musulunci dake zamanta a Kofar Kudu karkashin mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ta baiwa wani mai sana’ar durin Iskar Gas a Unguwar Tudun Wuzirci damar cigaba da sana’arsa biyo bayan bazanar dakatar da sana’ar da makotansa suka yi.*
Tunda farko mai sana’ar ta durin Iskar Gas wanda yaki amincewa a nadi muryarsa ya shigar da kara gaban Kotu yana bukatar Kotu ta bashi damar cigaba da sana’ar sa sannan kuma ta bashi kariya domin gudun abunda kaje yazo a unguwar ta Tudun Wuzirci.
Sai dai makotan nasa da yake kara a zaman Kotun na yau wadanda suma suka ki yadda mu fadi sunansu da muryarsu bayan alkali ya waiwaye su sun shaidawa masa cewa dama ya ajiye wata tireda ne a layi kuma ya dauketa daga baya a don haka su ba suda wani ja akansa, tun da ya magantu da kan sa.
Mai shari’a Ibrahim Sarki Yalo ya waiwayi wanda yake kara cewa ko yana da shaidar yin wannan sana’a daga wajen hukumomi, Inda ya gabatar da shaidu guda biyu ciki har da shaidar izinin hukumar kashe gobara ta jihar Kano.
Bayan kammala sauraron bangarorin biyu Sarki Yola ya baiwa mai sana’ar umarnin cigaba da sana’arsa a wajen kasancewar yana da takaddun shaidar yin sana’ar tasa.
Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa mai sharia Sarki Yola ya gargadi makotan da wanda yake sana’ar dasu zauna lafiya da juna kuma wanda yake sana’ar ya kiyaye ka’idoji domin kaucewa hadarin tashin gobara a gurin.
You must be logged in to post a comment Login