Labarai
Kotu ta yanke wa fiye da mutane 200 hukuncin daurin rai da rai
Kotu ta yanke wa fiye da mutane dari biyu da ta samu da aikata ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya hukuncin kisa da kuma daurin rai da rai.
Hakan na kunshe ne ta cikin wani rahoto da sashen yada labarai na ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na kasar nan ya fitar a jiya Lahadi bayan kammala shari’ar rukuni na shida na wadanda ake tuhumar.
Rahoton, ya ce, an fara gudanar da shari’ar ne daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Disamban shekarar nan ta 2024 da muke ciki inda aka gudanar da shari’u guda dari biyu da talatin da bakwai.
Ofishin, ya kara da cewa, baya ga wadanda kotu ta yanke wa hukuncin kisan, da kuma wadanda za su yi zaman daurin rai da rai, akwai wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru daga ashirin zuwa saba’in la’akari da nauyin irin laifin da mai laifin ya aikata.
Haka kuma rahoton, ya bayyana cewa, alkalan manyan kotunan tarayya biyar ne suka gudanar da shari’un rukuni-rukuni a gidan gyaran hali na Kainji.
You must be logged in to post a comment Login