Labarai
Kotu ta yankewa wani soja daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali
Wata kotu a kasar Chadi ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 kan wani Janar na soji da wasu masu mukamin Kanar guda 2 da kuma shugaban hukumar leken asiri saboda samun su da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Libya.
Wata majiya ta ce a watan Janairu ne aka kama mota makare da kwayar tramadol katan 246 da kudinsa ya kai Dala miliyan 21 a lokacin da ake safarar sa zuwa Libya.
Mai gabatar da kara Youssouf Tom, ya ce daga cikin mutane 11 da aka yi wa shari’ar, kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru 10-10 a kan mutane 6, yayin da sauran suka samu shekaru 4 zuwa 5.
Kotun ta kuma bukaci wadanda aka daure su biya tara tsakanin Dala Amurka 25,000 zuwa 50,000.
You must be logged in to post a comment Login