Labarai
Kotun ɗaukaka ƙara za ta sanya ranar yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta ce, za ta sanya ranar yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya shigar kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yi a baya na ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Idan za a iya tunawa, kotun mai alƙalai uku karkashin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta kori soke nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 20 ga watan Satumban bana bayan ta rage kuri’u 165,663 daga na gwamnan bisa samun su babu Sitamfi da kwanan wata.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, inda ta ce ya samu kuri’u 1,019,602 inda ya doke Gawuna wanda ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai kotun da ta amince da APC, ta soke nasarar ta Abba Kabir, inda ta kara da cewa sama da takardun ƙasa kuri’a 160,000 INEC ba ta sanya hannu ko tambari a kansu ba.
Haka kuma ta ƙara da cewa, An rage kuri’Un Abba Kabir Yusuf zuwa 853,939 yayin da kuri’u Ganuwa kuma suka kasance 890,705, don haka gwamnan ya shigar da kara a gaban kotun daukaka karar.
A zaman kotun na yau Litinin, ta ce, ta saurari lauyoyin ɓangarorin biyu, kuma nan gaba kaɗan za ta sanar da ranar yanke hukunci.
You must be logged in to post a comment Login