Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun daukaka kara a Kano ta jingine hukuncin nasarar da Jibrin Ismail Falgore ya yi

Published

on

Kotun daukaka kara dake zamanta a nan Kano ta jingine hukuncin da kotun sauraron karar zabe ta yi ranar 24 ga watan Yulin da ya gabata da ta yanke hukuncin cewa Jibrin Ismail Falgore ne ya yi nasara a zaben majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Rogo.

Da yake yanke hukuncin mai shari’a Abubakar Datti Yahaya wanda ya jagoranci alkalan kotun daukaka kara, ya baiwa daya daga cikin alkalan kotun damar karanta hukuncin, inda mai sharia H. A. O Abiru ya bayyana cewa lauyan dan takarar jam’iyyar PDP Barista Ibrahim Garba Waru ya gaza gamsar da kotu da kwararan hujjoji masu inganci a bisa rashin barin aiki kafin shiga takara.

A saboda haka ya zuwa yanzu dan takarar jam’iyyar APC Magaji Dahiru Zarewa ne a matsayin mai wakiltar karamar hukumar Rogo a majalisar dokokin jihar Kano.

Wakilinmu Bashir Muhammad Inuwa ya yi kokarin jin ta bakin lauyan PDP da ya wakilci Jibrin Ismail Falgore, amma bai ce komai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!